IQNA

Arbaeen 2023: Masu ziyara  Suna yin tattaki zuwa Karbala

KARBALA (IQNA) – Dubban maziyarta  ne ke amfani da hanyar da aka fi sani da “Tariq al-Ulama” don tafiya birnin Karbala mai alfarma domin halartar tarukan Arbaeen.

Suna tafiya a kan hanya mai ban sha'awa, mai tsawon kilomita 90 kuma tana a gefen kogin Euphrates. Wannan tafarki mai daraja ya kasance a tarihi da manyan malamai da dama suka bi , wadanda su ma suka yi tattaki zuwa Karbala da kafa.